Home / Big News / RA’AYI: Yunƙurin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Da Sarrafa Auduga Ta Zamfara, Gwamna Lawal Ya Cancani Yabo

RA’AYI: Yunƙurin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Da Sarrafa Auduga Ta Zamfara, Gwamna Lawal Ya Cancani Yabo

 

Fassarar Mahdi Musa Muhammad

A da, Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da suka yi fice wajen noman auduga a Nijeriya. Wannan ya sa aka kafa masana’antun sarrafa auduga da na yadi da dama, har ta zama ɗaya daga cikin cibiyoyin sarrafa auduga mafi girma a ƙasar.

Sai dai a yau, wannan ɗaukakar ta zama tarihi. Noman auduga ya ragu matuƙa, haka kuma sauran harkokin noma a jihar. Babban abin da ya jawo hakan shi ne matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar tsawon kusan shekaru ashirin, tare da ƙarancin ingantattun iri da manoma za su shuka.

Ko manoman da suka ci gaba da noma duk da matsalolin tsaro, sun fuskanci ƙarancin amfanin gona da kuma raguwar ingancin audugar da suke nomawa.

Sakamakon haka, masana’antun yadi da masu sarrafa auduga sun fara durƙushewa saboda rashin isasshen auduga, wadda ita ce babban kayan aikin da suke amfani da shi. Hakan ya sa dubban mutane suka rasa ayyukansu, daga manoma zuwa ma’aikatan masana’antu da sauran masu sana’o’in da suka dogara da harkar auduga.

Durƙushewar wannan fanni ta ƙara ta’azzara matsalolin rashin aikin yi, talauci da rashin tsaro a jihar.

Abin tambaya shi ne, me ya sa jihar da a da take da masana’antun sarrafa auduga guda 15, waɗanda kowacce ke ɗaukar ma’aikata sama da mutum 200, yanzu ta rage da ƙasa da guda biyar?

Me ya sa aka bari Kamfanin Zamfara Textile Limited (ZTL), wanda Marigayi Sir Ahmadu Bello ya ƙaddamar a shekarar 1965 kuma yake ɗaukar ma’aikata kusan 3,000, ya lalace har aka rufe shi a shekarar 2004?

Wane dalili ne ya sa wannan masana’anta da ta kasance ginshiƙin tattalin arzikin dubban iyalai ta durƙushe? Kuma me gwamnati ke yi domin dawo da ita bakin aiki?

Domin warware wannan matsala, wajibi ne gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su gano ainihin abubuwan da suka jawo durƙushewar wannan masana’antu tare da ɗaukar matakan magance su.

Dole ne a yi tambaya kan rawar da rashin tsaro, ƙarancin ingantattun iri da kuma shigo da yadudduka daga ƙasashen waje ke takawa wajen lalacewar wannan fanni. Haka kuma, ya kamata a tabbatar wa manoma da samar musu da ingantattun iri masu yawan amfanin gona. Sannan gwamnati ta ɗauki tsauraran matakai wajen rage shigo da kayan yadi daga ƙetare.

A kwanakin baya, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana aniyarsa ta farfaɗo da masana’antun yadi da sarrafa auduga a jihar domin samar da ayyukan yi da rage talauci.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ziyara da ya kai yankin masana’antu da ke kusa da birnin Cotonou a Jamhuriyar Benin, inda ake sarrafa auduga, goro, waken soya da sauran albarkatun noma zuwa kayayyakin da aka gama ƙerawa.

A ‘yan shekarun nan, Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta nuna ƙuduri wajen farfaɗo da sassan tattalin arziƙin jihar da suka yi baya. Daga inganta ababen more rayuwa zuwa ƙoƙarin bunƙasa harkokin noma da masana’antu, gwamnatin na ci gaba da shimfiɗa tubalin dawo da martabar Zamfara a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin samar da albarkatun noma da masana’antu a Arewacin Najeriya. Wannan ƙuduri ya ƙara ƙarfafa fatan cewa masana’antar auduga da masaku za su sake dawowa da ƙarfi idan aka ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da aka fara.

A cewarsa, abin da ya gani ya ƙara masa ƙwarin gwiwar ganin an dawo da irin wannan ci gaba a Zamfara.

Haƙiƙa, idan aka samar da ingantacciyar manufa daga gwamnati, aka gina ababen more rayuwa, sannan aka samu haɗin gwiwar masu zuba jari masu zaman kansu, za a haɗa manoma da masana’antu kai tsaye. Wannan zai rage fitar da ɗanyen kayan noma zuwa ƙasashen waje tare da samar da dubban ayyukan yi a bangaren noma da masana’antu.

Masana’antar yadi ta Zamfara, wadda a da ta kasance tushen aikin yi ga dubban mutane, na buƙatar a dawo da ita cikin gaggawa. Babu shakka wannan fanni na da ƙarfin samar da ayyukan yi masu yawa.

A matakin ƙasa kuwa, Nijeriya na buƙatar sabon tsari na farfaɗo da masana’antar Auduga, Yadi da Tufafi (CTG), domin wannan fanni na iya samar da fiye da ayyukan yi miliyan 1.5, tare da ƙarfafa masana’antu da kuma haɓaka fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.

Shekaru na sakaci, rashin ingantaccen tsari da kuma dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje ne suka jawo koma bayan wannan masana’anta.

Idan gwamnatin jihar Zamfara ta aiwatar da shirinta yadda ya kamata tare da haɗa hannu da shirin Gwamnatin Tarayya na bunƙasa sarkar masana’antar Auduga, Yadi da Tufafi, za a dawo da martabar wannan fanni, tare da gina cikakkiyar sarkar samar da kayayyaki daga noma zuwa ƙera tufafi da za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya.

Don haka, abin da ake buƙata yanzu shi ne gwamnatin Dauda Lawal ta mayar da alkawarinta zuwa aiki. Ta tanadi kuɗi da ƙwararrun ma’aikata, sannan ta ɗauki matakan magance matsalar rashin tsaro, domin ba tare da zaman lafiya ba ba za a iya farfaɗo da noman auduga ko masana’antun da suka dogara da shi ba.

Idan aka cimma wannan buri, Zamfara da Nijeriya baki ɗaya za su amfana matuƙa. Za a samar da dubban ayyukan yi, tattalin arziki zai bunƙasa, kuma rashin aikin yi da ke ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro zai ragu sosai.

About andiya

Check Also

Dangote, Sinoma Sign $800 Million MOU to Expand Itori Cement Plant Capacity to 12 MTA

…Expansion Project to Strengthen Nigeria’s Position as a Major Cement Export Hub   Dangote Industries …

Leave a Reply

Your email address will not be published.