Home / Labarai / HARIN ’YAN BINDIGA: Gwamna Lawal Ya Ziyarci Bungudu, Ya Sake Jaddada Matsayar Gwamnatinsa Kan Yaƙi Da Ta’addanci

HARIN ’YAN BINDIGA: Gwamna Lawal Ya Ziyarci Bungudu, Ya Sake Jaddada Matsayar Gwamnatinsa Kan Yaƙi Da Ta’addanci

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake nanata cewa gwamnatinsa ba za ta taɓa shiga tattaunawa ko yin sulhu da ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ba, yana mai jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin murƙushe matsalar rashin tsaro a jihar.

A ranar Alhamis, gwamnan ya kai ziyarar jaje Ƙaramar Hukumar Bungudu, domin ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ‘yan bindiga ya shafa, da Masarautar Bungudu, da kuma al’ummar yankin baki ɗaya.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, ziyarar ta fara ne a fadar Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, inda Gwamna Lawal ya bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara.

Ya ce, ya je Bungudu ne domin jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa ‘yan uwansu, da Sarkin Bungudu, da kuma ɗaukacin al’ummar yankin sakamakon harin ‘yan bindigar da ya afku a makon da ya gabata.

Gwamnan ya bayyana cewa abin da ya faru wata jarrabawa ce daga Allah Maɗaukakin Sarki, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa za a yi nasarar shawo kan matsalar.

Ya ce, gwamnatin jihar na ci gaba da karkata dukkan ƙarfinta da albarkatunta wajen kawo ƙarshen ta’addanci da ayyukan ‘yan bindiga.

Gwamna Lawal ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da nuna haƙuri, yana mai cewa yaƙi da rashin tsaro na buƙatar jajircewa tare da yawaita addu’a.

Ya yi addu’ar Allah Ya bai wa iyalan mamatan juriyar wannan babban rashi, tare da roƙon Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasa rayukansu.

Har ila yau, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da kula da waɗanda suka jikkata, tare da yin duk mai yiwuwa domin ganin an kuɓutar da duk mutanen da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.

Da yake mayar da martani, Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru, ya gode wa Allah bisa bai wa Jihar Zamfara gwamna da ke nuna damuwa da halin da jama’a ke ciki tare da ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Sarkin ya ce kasancewarsa mamba a Kwamitin Tsaro na Jihar Zamfara, yana sane da irin ƙoƙarin da gwamnan ke yi wajen yaƙi da ‘yan bindiga, yana mai bayyana tabbacin cewa za a yi nasarar shawo kan matsalar.

Ya kuma gode wa gwamnan bisa ziyarar jajen, yana mai cewa hakan ya ƙara wa al’ummar Bungudu ƙarfin gwiwa.

Yayin ziyarar tasa, Gwamna Lawal ya kai ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Bello Umar Bungudu, da sauran iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a harin.

About andiya

Check Also

Gwamna Uba Sani Ya Raba wa Mutanen Alhuhuda Filayen 92 A Zariya

  Daga Imrana Abdullahi A wani babban taron da aka yi a dakin taron makarantar …

Leave a Reply

Your email address will not be published.