Rahotanni daga Jihar Kaduna n bayanin cewa sama da mutane 20 ne aka sace, aka kuma kashe mutum 1 a lokacin wani harin da aka kai a unguwar Danbushiya da ke wajen harabar rukuni gidaje na Millenium City, a karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna. Wani Shaidan gani da ido …
Read More »Ina Son A Kaini Kara Kotu – Mahadi Shehu
Imrana Abdullahi Fitaccen dan kasuwa Alhaji Mahadi Shehu ya yi kira ga dukkan wanda yake gani ya fadi wani ABU dangane da badakalar kudin da ake yi a Jihar katsina bai gane ba da ya kai shi kara kotu domin a bi masa hakki a kotu. Mahadi Shehu ya bayyana …
Read More »Allah Ya Yi Wa Barista Inuwa Abdulkadir rasuwa
Imrana Abdullahi Bayanan da muke samu daga Jihar Sakkwato mahaifar marigayin sun tabbatar da rasuwarsa a safiyar yau Litinin. Ya rasu yana da shekaru 54 kuma kafin rasuwarsa ya taba zama minista a tarayyar Nijeriya kuma ya rike matsayin mukamin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso Yamma.
Read More »An Samu Barnar Ruwa A Kaduna
Imrana Abdullahi Sakamakon ruwan sama tare da Iska mai tsanani da aka yi a cikin garin Kaduna ya haifar da asara a gidaje inda rufin gidajen ya lalace, an kuma samu matsalar karyewar turakun wutar lantarki da katsewar wayoyin wutar lantarki. Lamarin dai ya faru ne a unguwannin layin Sardauna …
Read More »Za Share Dukkan Yan Ta’adda Baki Daya – Masari
Imrana Abdullahi Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa al’ummomin kananan hukumomi takwas da suke iyaka da Dajin rugu suna cikin halin zaman dar-dar, zullumi da rashin tabbas sakamakon yadda ‘yan ta’adda suke kai masu hare-hare da manyan bindigogi wanda ke zama sanadiyyar rasa rayuka da dukiyoyi. Gwamnan ya bayyana …
Read More »A Mayar Da Liman Musa Tanimu Zariya – Al’ummar Unguwar Rimi
Imrana Abdullahi Al’ummar Unguwar Rimi da ke cikin garin Kaduna a Arewacin tarayyar Nijeriya sun bukaci a mayar da Liman Musa Tanimu Zariya a kan Limancinsa na masallacin babban masallacin unguwar Rimi ( central mosque) da ake kira masallacin iyaye da Kakanni. Al’ummar ta bakin daya daga cikin wadanda suka …
Read More »Babban Alkalin Jihar Kogi, Mai Shari’a Nasiru Ajana Ya Rasu
Imrana Abdullahi Rahotannin da ke Iske mu daga garin Abuja na cewa babban mai shari’a na Jihar Kogo a Arewacin tarayyar Nijeriya, mai Shari’a Nasiru Ajanah ya rasu a yau da safiyar Lahadi a Abuja. Bayanan da ke Iske mu sun bayyana cewa ya rasu ne bayan ya yi fama …
Read More »Sanata Hadi Sirika Ya Zagaya Tashoshin Jiragen Sama
Mustapha Abdullahi A kokarin ganin an dawo da zirga zirgar tashi da sauka a tashoshin Jiragen kasar tarayyar Nijeriya ministan ma’aikatar kula da tashi da saukar Jiragen Sama Sanata Hadi Sirika ya zagaya tashoshin da aka bude domin ganin yadda lamarin ke gudana. Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na …
Read More »Mazauna Kasar Saudiyya Ne Kawai Za Su Yi Aikin Hajji
Mahukuntan kasar Saudiyya sun bayyana cewa yannkasar ne kawai za su yi aikin Hajjin Bana tare da yan asalin wadansu kasashen waje da suke zaune a cikin kasar ne za a bari su aiwatar da aikin hajjin na Bana. Cikin wata sanarwa da ma’aikatar aikin Hajji kasar ta fitar …
Read More »Gidauniyar Zaman Lafiya ta horar da mata hanyoyin kasuwanci tare da tallafa musu da jari
Gidauniyar Zaman Lafiya ta Duniya (GPF) ta horar da mata 40 hanyoyin kasuwanci inda ta baiwa kowace jarin naira dubu 10 don fara aiwatar da kananan sana’o’ a masarautar Kaninkon da ke karamar hukumar Jama’a ta jihar Kaduna. Yayinda yake jawabi a wajen bayar da horon da aka gudanar a …
Read More »
THESHIELD Garkuwa